Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Hukumar Sojin saman Najeriya, NAF, ta bayyana cewa binciken da ta gudanar ya nuna mata cewa jirgin yakinta Alpha Jet (NAF475) da ta bace a sararin samaniya yayi hadari.

Kakakin hukumar NAF, Edward Gabkwet, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da safiyar Juma’a. 2 ga Afrilu, 2021.

Gabkwet ya bayyana cewa akwai matuka biyu cikin jirgin kuma ya bayyana sunayensu matsayin, FL John Abolarinwa da FL Ebiakpo Chapele.

“Rahoton bincike da hukumar NAF ta tattaro ya nuna cewa jirgin NAF475 da ta bace da matuka biyu ranar 31 ga Maris 2021 ta samu hadari,” yace.

Har yanzu ba’a san abinda ya haddasa hadarin ba kuma ba’a san inda matukan suke ba.Lamar yadda legit ta ruwaito,

“Har yanzu jirgi na nemansu kuma Sojojin kasa na bincikensu. A yanzu dai muna kyautata zaton za’a ganosu kuma a cetosu.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *