Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Bayan samun nasara a wasanni 4 da kunnen doki 1 daga cikin wasanni 5 da kungiyar kwallon kafa ta Giodano fc tayi a wasan yan rukuni na daya na gasar wasan kwallon kafa ajin matasa na daya kungiyar na daf da komawa rukunin wasan kwararru bayan samun nasara da tayi kan kungiyar Clever Warriors daci 3-2 a wasan karshe na rukuni a shiyyar Jos,

A tattaunawarsa da expressradiofm.com jim kadan bayan kammala wasan shugaban kungiyar Giodano fc Jamilu Wada cewa yayi ” Alhamdulillah Alhamdulillah mungode wa Allah kuma ina yanawa yan wasa, masu Horarwa da magoya bayan mu wadanda sukai ta aiki ba dare ba rana dan ganin mun sami wannan nasara Allah mungode ”

ayake karin haske kan wasan karshen da kungiyar Clever cewa yayi ya zama wajibi na yaba musu saboda irin kwazo da  Da’a da suka nuna a wasan, inda yace 3-2 alamace ta cewa suma sunason samun wannan damar to amma mu Allah ya bawa saboda haka ina yi musu fatan alheri a nan gaba, kuma ina jinjinawa Shugaban kungiyar  Najib Kurawa bisa kokarinsa na hada team irin wannan, babu shakka wannan team din Clever Warriors suna da kyakykyawar makoma nan gaba,  kuma zasu Shiva tarihi na masu son sauya fasalin wasan kwallon kafa a jihar Kano da kasa baki daya inda ya kara da cewa ” Na dade banga Club da yan wasa matasa masu Da’a da kwazo irin Clever Warriors ba ina yi musu fatan alheri,” kuma nan gaba kadan zasu bada mamaki,

Dangane da shafe wasanni 5 ba tare da anyi nasara a kan kungiyarsa ba Jamilu Wada cewa yayi ” Ita Giodano haka take idan mukasa abu a gaba da gaske mukeyi, na sha fada maka cewa Giodano Giodano ce kuma ina alfahari da ita a ko’ina saboda dogon tarihinta da nasarorinta” kan kalubalen dake gaban kungiyar na wasan karshe Jamilu cewa yayi ” Da Allah muka dogara kuma shine zai bamu sa,’a kamar yadda ya bamu tunda fari kuma inshaallah jihar Kano sai ta samu wannan gurbin, dama na tane ”

Kungiyar Giodano ta jagoranci yan rukuni na daya da suka fafata a shiyyar Jos da maki 13 daga wasanni biyar data buga tarihin da yayi kama da wanda tayi a jihar Gombe shekaru 4 da suka gabata inda ta samu tikiti shiga rukunin Kwararru na kasa NNL

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *