Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta clever warriors dake kano Najib Kurawa yace abin alfahari ne irin nasarori da kungiyar ta samu a wasannninta a gasar ajin matasa rukuni na daya na bana da aka fara a fadin kasar nan, kungiyar Clever na fafatawa a shiyyar Plateau tsakanin manyan kungiyoyi 9 da suka goge a gasar cikinsu harda wadanda suka fado daga rukunin kwararru in banda kungiyar ta Clever dukkanin kungigyoyi 8 da suke shiyyar kumgiyoyine da suka dade suna buga gasar

Yin nasara tsakanin kungiyoyi irinsu Giodano, Aklesondi, Zabgai da saurarnsu ga matashiyar kungiya irin tamu abin ayabawa yan wasan da masu horar dasu ne,

Najib yace ” yan wasanmu sunyi kokari kuma zamuci gaba dayin kokari dan ganin munkara samun nasara a wasanninmu na gaba ”

” Na fada ba kallo munkazo ko kare matsayi ba, munzo ne muyi gogayya da kowace kungiya tare da neman gurbi na gasar kwararru kuma har yanzu kungiyar mu ta Clever Warriors nada dama kuma zamu ci gaba da nema har zuwa karshen gasar”

“Bana shakkar yan wasana mun shirya tunkarar kowane irin kalu bale” inji Najib Kurawa

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *