A yayin da jihohin arewa maso yamma ke fama da rikice rikice da rashin zaman lafiya sai gashi kwatsam Alhaji Sirajo Maikatako, Kwamishinan aikin hajji na jihar Zamfara ya yi murabus
Ya bayyana hakan ne yayin yi wa ‘yan jam’iyyar APC jawabi a ranar Alhamis a babban birnin jihar
A cewarsa, yana da yakinin jam’iyyar APC ce za ta yi nasarar lashe zaben 2023 da za a yi a jihar
Kwamishinan aikin hajji, Alhaji Sirajo Maikatako, ya yi murabus. Ya bayyana hakan ne a wani taron ‘yan jam’iyyar APC da aka yi a Gusau ranar Alhamis, Daily Trust ta wallafa.
Ya bayyana yakininsa inda yace jam’iyyar APC ce za ta lashe kaf kujerun jihar a zaben 2023, har yana cewa ya yi aiki ne karkashin jam’iyyar PDP a matsayin shugaba ba dan siyasa ba.
“Ina farin cikin sanar da canja shekata daga shugabanci a karkashin jam’iyyar PDP. Na yi hakan ne don nuna matukar goyon baya ga shugabana a harkar siyasa, Sanata Kabiru Marafa don samun wanzuwar kwanciyar hankali da hadin kan jam’iyyar APC.