Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kai hari yankin Shagari quarters dake karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina, inda suka kashe shugaban ‘yan sa kai dake wurin, Ali Bahago, bayan musayar wuta da suka yi.

‘Yan bindigar sun yi garkuwa da wani Mr. Alex, ma’aikacin banki da yaran wani tsoho Hassan, wanda take a wurin ya fadi ya mutu.

Wani mazaunin quarters din wanda babu abinda ya faru dashi a ranar, Sagir Mohammed, ya sanar da ThisDay a ranar Juma’a cewa ‘yan bindigan sun shiga quarters din da misalin 11:15pm ranar Alhamis, 11 Fabrairu, kuma sun shafe mintuna 30, inda suka bar ma’aikatan da dama da miyagun raunuka.

Yan bindiga sun kai hari Shagari quarters a ranar Alhamis inda suka kashe Alhaji Ali Bahago, shugaban ‘yan sa kan wurin. Ya je ne don ya cece mu daga wurin ‘yan bindiga amma sun kashe shi sakamakon musayar wutar da suka yi,” a cewarsa.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *