Rundunar sojojin ruwan Najeriya ta fitar da wani sanawar dauke da hotuna da sunayen wasu jami’anta da suka tsere daga aiki tana mai neman duk wanda ke da bayani da zai taimaka a kamo su ya tuntubi ofishinta ko na ‘yan sanda mafi kusa.
The Punch ta ruwaito cewa an wallafa sanarwar ne a hedkwatar rundunar sojin ruwan da ke binrin tarayya Abuja.
Sanarwar ta kuma wajabtawa dukkan jami’an rundunar da ke da bayannan game da jami’an da suka tsere su kamo su ‘idan ba haka ba a dauke su a matsayin wadanda suke taimaka musu’.
Duk da cewa ba a bada dalilin bacewar jami’an ba, an ruwaito cewa sojojin galibinsu masu aiki a jiragen ruwa na rundunar a kasashen waje sun tsere ne a lokacin da jiragensu suka isa gabar Turai.