Contact Information

114 Lamido Cresent, Giginyu 700213, Kano

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyoyi sama da arbain ne zasu fafata a sabuwar gasar wasan kwallon kafa da hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano ta bullo da ita a karon farko a tarihi,

Kungiyoyin da zasu fafata gasar kungiyoyi ne dake bugawa a rukunin ajin matasa na kasa da ake kira Nationwide league, tun a karshen shekarar 2019 akaso.gudanar da gasar amma hakan bai yiwuba inda kuma cutar Corona a shekara ta 2020 ta tsaida harkokin duniya ciki harda wasan kwallon kafa.

A tattaunawar sa da wakilin express radio online a  yayin wani taro da kungiyoyin dake wakiltar jihar kano a gasar rukunin matasa ta kasa shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Sharu Rabiu Ahlan ya bayyana dalilin sanya gasar da cewa zata motsa tare da shirya kungiyoyin tunkarar wasan ajin matasa ta kasa inda ya Kara da cewa wasannin zasu taimakawa kungiyoyin fsrfadowa daga mashashsharar Corona data tsaida kungiyoyin kimanin watanni bakwai,

Sharu Ahlan ya kara da cewa laakari da yawan kungiyoyin da jihar kano ke dasu akwai bukatar samar da irin wadannan gasa dan bawa kungiyoyin damar da zasu shirya gabanin wasannin su,inda yace wannan wasane da zai zama Dan ba na bunkasa wasan kwallon kafa a jihar, kuma wasan zai sauya tunanin kungiyoyin ta yadda zasu gudanar da tsarin Kungiyoyin su

nda yace Unity Cup zai zama mabudin samun hadin kan kungiyoyin jihar Kano.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *